logo

HAUSA

Sin ta habaka shigar da kayayyaki cikin shekaru uku a jere

2022-07-15 14:33:20 CMG Hausa

Bisa kididdiga da babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ta fitar, a rabin farko na shekarar 2022, darajar kayayyakin da kasar ta shigo da su daga kasuwar ketare ya kai yuan triliyan 8.66, wanda ya karu da kashi 4.8 cikin dari, a kan na makamancin lokacin a bara. Bugu da kari, shekaru uku ke nan a jere da wannan adadi ke ci gaba da habaka.(Safiyah Ma)