logo

HAUSA

GDPn farkon watannin 6 na bana a kasar Sin ya karu da kashi 2.5%

2022-07-15 13:22:59 CMG HAUSA

 

Yau Juma’a da safiya, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa na kasar Sin ya yi taron manema labarai, don bayyana yadda tattalin arzikin kasar yake a farkon watanni 6 na bana.

Alkaluma na nuna cewa, yawan GDPn a kasar a farkon watanni 6 na bana ya kai kudin Sin Yuan biliyan 56264.2, wanda ya karu da kashi 2.5% bisa na makamancin lokaci na bara. Daga cikinsu, sha’anin gona da na masana’antu da ba da hidimma, sun samu karuwa da yawansa ya kai Yuan biliyan 2913.7 da Yuan biliyan 22863.6 da Yuan biliyan 30486.8. Wanda ya karu da kashi 5.0% da kashi 3.2% da 1.8% bisa na makamancin lokaci na bara.

Ban da wannan kuma, a cikin watannin Afrilu zuwa Yuni, GDPn kasar ya kai Yuan biliyan 29246.4, wanda ya karu da kashi 0.4% bisa na makamancin lokacin bara. Daga cikinsu, sha’anin gona da na masana’antu na samun karuwar Yuan biliyan 1818.3 da Yuan biliyan 12245, wanda ya karu da kashi 4.4% da kashi 0.9% bisa na makamancin lokaci na bara, inda a sha’anin ba da hidimma aka samu karuwar Yuan biliyan 15183.1, wanda ya ragu da kashi 0.4%. (Amina Xu)