logo

HAUSA

Cinikayya tsakanin Sin da kasashen “Ziri daya da hanya daya” tana karuwa

2022-07-15 14:35:06 CMG Hausa

Bisa kididdiga ta baya-bayan nan da babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ta fitar, a rabin farko na shekarar 2022, darajar kayayyakin shige da fice tsakanin Sin da kasashen da suka shiga shawarar “Ziri daya da hanya daya ” ta kai yuan triliyan 6.31, wadda kai kashi 31.9 cikin dukkanin kayayyakin shige da fice na kasar a lokacin. Cinikayya tsakanin sassan biyu tana kara habaka. (Safiyah Ma)