logo

HAUSA

Kwamitin sulhun MDD ya tsawaita haramcin fitar da mai daga kasar Libya

2022-07-14 10:12:14 CMG Hausa

 

            

Kwamitin sulhun MDD jiya Laraba, ba tare da mahayya ba, ya amince da wani kuduri na tsawaita dokar hana fitar da man fetur ba bisa ka'ida ba, da suka hada da danye da tataccen man fetur daga kasar Libya na tsawon watanni 15, har zuwa ranar 30 ga watan Oktoban shekarar 2023.

Kudurin mai lamba 2644, ya kuma tsawaita wa'adin kwamitin kwararru da ke taimakawa takunkumin da kwamitin ya kakabawa kasar har zuwa ranar 15 ga Nuwamban shekarar 2023.

Kudurin ya bukaci dukkan kasashe mambobin MDD, da su martaba dukkan takunkuman haramcin shigar da makamai, da hana zirga-zirga da kwace kadarorin da aka sanyawa Libyan, sannan ya yi kira ga daukacin kasashe mambobin kwamitin, da kada su tsoma baki a rikicin kasar Libiya, ko daukar matakan da za su kara ta'azzara rikicin.

Bugu da kari, kwamitin ya bukaci dukkan bangarorin kasar, da su aiwatar da cikakkiyar yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a ranar 30 ga watan Oktoban shekarar 2020, tare da yin kira ga kasashe mambobin majalisar, da su mutunta tare da goyon bayan ganin an aiwatar da cikakkiyar yarjejeniyar, gami da janyewar dukkan sojojin kasashen waje da na haya daga Libya ba tare da bata lokaci ba. (Ibrahim)