logo

HAUSA

Za A Shirya Babban Taron Muhimman Al’adun Gargajiya Na Aikin Gona Na Duniya A Kasar Sin

2022-07-14 10:42:26 CMG Hausa

A shekarar 2002 ne hukumar kula da abinci da aikin gona ta MDD(FOA) ta gabatar da wata shawara dangane da muhimman al’adun gargajiya na aikin gona na duniya. A bana ne, aka cika shekaru 20 da gabatar da wannan shawara. Daga ranar 17 zuwa 19 ga wata, za a gudanar da babban taron muhimman al’adun gargajiya na aikin gona na kasa da kasa a gundumar Qingtian ta lardin Zhejiang da ke gabashin kasar Sin, babban taken taron shi ne, kiyaye al’adun gargajiya na aikin gona tare da kara azama kan farfadowar yankunan karkara daga dukkan fannoni.

Muhimman al’adun gargajiya da suka shafi aikin gona na kasa da kasa, wasu tsare-tsaren gargajiya ne na aikin gona, wadanda suke da daraja sosai a fannin al’adu da tarihi, wadanda kuma suka kasance a matsayin abubuwan koyi a fannin aikin gona na zamani, inda aka hada aikin shuke-shuke, aikin kiwon dabbobi, kiwon kifi da aikin sarrafawa waje guda. Ya zuwa yanzu, akwai muhimman al’adun gargajiya 18 da suka shafi aikin gona a kasar Sin, adadin dake kan gaba a duniya.

Shugaban sashen hadin gwiwa da kasashen duniya na ma’aikatar noma da yankunan karkara ta kasar Sin, Sui Pengfei ya bayyana fatan ganin an yi amfani da babban taron, a matsayin dandalin musayar ra’ayoyi da hadin gwiwa tsakanin sassa daban daban,da cimma matsayi guda tsakanin kasa da kasa kan daukar matakin bai daya, da fadada ayyukan farfado da yankunan karkara, da yayata da gadon al’adun aikin gona, da yin koyi da juna. Sui ya ce, “A yayin babban taron, za a yi musayar ra’ayoyi kan matakan da kasashen duniya suke dauka a fannonin yin amfani da al’adun gargajiya na aikin gona, wajen kyautata tsarin samar da abinci, da kara samar da ci gaba mai dorewa a yankunan karkara, da kyautata zaman rayuwar manoma, a kokarin ganin an wadatar da yankunan karkara tare. Muna fatan za a yi amfani da babban taron, wajen kara tuntubar juna don fito da sabbin dabaru a fannoni masu ruwa da tsaki.” (Tasallah Yuan)