logo

HAUSA

Biden ya isa Isra’ila a bangaren ziyarar sa a yankin Gabas ta Tsakiya

2022-07-14 10:23:19 CMG Hausa

Shugaban Amurka Joe Biden, ya isa Isra’ila da yammacin jiya Laraba, kasar da ta zamo zangon farko a ziyarar da ya fara a Gabas ta tsakiya, kuma ziyararsa ta farko a yankin tun hawansa karagar mulkin Amurka. Yayin wannan ziyara, zai tattauna da shugabannin kasashen Isra’ila, da na al’ummar Falasdinawa, da na masarautar Saudiyya.

Shugaban kasar Isra’ila Issac Herzog, da firaministan kasar Yair Lapid, da ministoci da ’yan majalissar dokokin kasar, sun yiwa Mr. Biden tarbar alfarma, a filin jirgin sama na Ben Gurion dake wajen birnin Tel Aviv. Ya kuma saurari bayani game da harkar tsaro, mai nasaba da fasahar Isra’ila ta kariya daga makaman roka masu karin ingani, irin su na baya-bayan nan da Isra’ilan ta kera domin tsaron sararin samaniya.

Yayin da yake tsokaci cikin jawabinsa, firaminista Lapid, ya bayyana shugaba Biden a matsayin daya daga muhimman aminai da Isra’ila ta taba yi a tarihi. Lapid ya ce "Mun tattauna game da gina sabon salon wanzar da tsaro, da raya tattalin arziki tare da sauran kasashen dake yankin Gabas ta tsakiya, biyowa bayan yarjejeniyar Abraham. Mun kuma tattauna game da bukatar sabunta kawancen kasa da kasa, wanda zai dakile shirin kasar Iran na samar da makaman nukiliya".

A nasa bangare, Mr. Biden ya ce alakar dake akwai tsakanin Amurka da Isra’ila na da zurfi, kuma a nan gaba, sassan biyu za su yi aiki tare, don ingiza dunkulewar Isra’ila a yankin na gabas ta tsakiya. (Saminu)