logo

HAUSA

Sin ta gargadi jirgin ruwan sojin Amurka game da shiga yankin ruwanta

2022-07-13 20:10:48 CMG Hausa

Rundunar sojin kasar Sin PLA, ta bayyana a yau Laraba cewa, ta bibiya tare da jan kunne jirgin ruwan sojin Amurka USS Benfold, bayan ya shiga yankin ruwa dake kusa da tsibiran Xisha, a tekun kudancin kasar Sin ba tare da izinin gwamnatin kasar Sin ba.

Wata sanarwa da kakakin rundunar soji ta kudancin kasar Sin, Tian Junli ya fitar, ta ce matakin na sojin Amurka, ya keta cikakken ‘yancin kasar Sin da muradunta na tsaro, da yin karan tsaye ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tekun kudancin Sin. Haka kuma, ya keta dokokin kasa da kasa da ka’idojin huldar kasa da kasa. (Fa’iza Mustapha)