logo

HAUSA

Takardar kudin Euro ya fado zuwa daidai da dalar Amurka

2022-07-13 09:46:39 CMG HAUSA

 

Rahotanni na nuna cewa, a karon farko cikin shekaru 20, takardar kudin Euro jiya Talata, ta sauko daidai da dalar Amurka, ma'ana dalar Amurka 1 na daidai da kudin euro daya.

Takardar kudin da kasashen tarayyar Turai 19 ke amfani da ita, ba ta taba fadowa ko yin kasa a fannin kimar musanya daidai da dalar Amurka ba, tun watan Disamba shekarar 2002.

Bayan samun wannan daidaito tsakanin takardun kudaden, farashin canjin Euro ya sake dagawa kadan. Da karfe 4 da mituna 20 na yamma, agogon yankin Turai, ana sayar da takardar kudin Euro a kan dalar Amurka 1 da centi 5 a kasuwar canji.

A cewar Ebrahim Rahbari, shugaban rukunin cibiyar dake sharhi kan binciken musayar kudade ta duniya mai suna Citigroup, takardar kudin Euro za ta ci gaba da faduwa ko da bayan ta fado kasa da dalar Amurka.

Wasu bayanai daga babban bankin Turai (ECB) na cewa, tun a farkon wannan shekara, takardar kudin euro ta fadi da kashi 10 a kan dalar Amurka.

A jiyan ma farashin mai ya fadi sosai, biyo bayan faduwar dalar Amurka, da kuma damuwar da ake da ita game da karancin bukatarsa a kasuwa. (Ibrahim)