logo

HAUSA

Xi ya yi murnar kafa kungiyar kasa da kasa kan kafar intanet

2022-07-12 19:12:49 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murnar kafa kungiyar kasa da kasa ta tattauna batutuwan da suka shafi kafar intanet.

Xi Jinping ya jaddada cewa, kafar intanet na da alaka da makomar bil adama. Kuma Sin ta shirya hada hannu da kasa da kasa wajen daukar kungiyar a matsayin wata muhimmiyar dama ta inganta tabbatar da kafar ta intanet ta kasance buddadiya mai cike da tsaro da tabbatar da adalci, kuma mai kwari da kuzari, ta yadda jama’a a fadin duniya za su amfana.

An gudanar da taron kaddamar da kungiyar ne yau, a birnin Beijing. (Fa’iza Mustapha)