logo

HAUSA

Xi Jinping ya amsa wasikar da matasan yankin Taiwan suka rubuta masa

2022-07-12 15:55:32 CMG HAUSA

 

Yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar da matasan yankin Taiwan da suka halarci dandalin matasan babban yanki da yankin Taiwan suka rubuta masa, ina ya karfafa musu gwiwar hadin kai don tabbatar da farfadowar al’ummar Sinawa baki daya.

An gudanar da wannan dandali karo na 20 ne a birnin Xiamen dake lardin Fujian daga jiya zuwa yau. A baya-bayan nan ne, matasan yankin Taiwan 50 da aka gayyata zuwa taron dandalin, suka rubutawa babban sakatare Xi Jinping wasika, inda suka bayyana yadda suke karatu da aiki da zaman rayuwa a babban yankin kasar Sin, da kuma aniyyarsu ta taka rawa wajen farfadowar al’ummar Sinawa da dinkuwar kasa baki daya. (Amina Xu)