logo

HAUSA

MDD: yawan al’ummar duniya zai zarce biliyan 8 a watan Nuwamba na bana

2022-07-12 11:22:25 CMG HAUSA

 

Ranar 11 ga wata, ranar ce ta yawan jama’a ta duniya, MDD ta gabatar da rahoto mai taken “hangen nesa kan yawan al’ummar duniya na shekarar 2022” a wannan rana cewa, yawan al’ummar duniya zai zarce biliyan 8 a watan Nuwamban bana.

Rahoton ya nuna cewa, tun daga shekarar 1950 zuwa yanzu, a karon farko, yawan haihuwa a kasashe da dama ya ragu matuka a cikin ’yan shekarun nan, yayin da karuwar al’ummar duniya ta ragu kasa da kashi 1% a shekarar 2020. An yi hasashen cewa, daga shekarar 2022 zuwa 2050, yawan al’ummar wasu kasashe ko yankuna 61, zai ragu kasa da kashi 1% ko fiye da haka. Haka kuma, a wannan lokaci kasashe 8 wato Kongo Kinshasa da Masar da Habasha da Indiya da Nijeriya da Pakistan da Philippines da Tanzaniya, za su samun karuwar mutane.

Rahoton ya kuma ce, matsakaicin tsawon rayuwar jama’a a duniya a shekarar 2019 ya kai shekaru 72.8, wanda ya karu da shekaru 9 bisa na shekarar 1990, amma adadin ya ragu zuwa shekaru 71 a shekarar 2021, sakamakon illar cutar COVID-19. Baya ga haka, a shekarar 2021, matsakaicin tsawon rayuwa a kasashe masu karancin ci gaba a duniya, shekaru 62 ne kawai, kasa da shekaru 7 na matsakaici na duniya. (Amina Xu)