logo

HAUSA

Kasar Sin za ta taimaka wa kamfanoni samun ci gaba mai inganci tare da taimakon kwalejoji da jami'o'i

2022-07-12 10:30:03 CMG HAUSA

 

Wata takardar sanarwar da ma'aikatar ilimi da ma’aikatar masana'antu da fasahar sadarwa da hukumar kula da mallakar fasaha ta kasar Sin suka fitar cikin hadin gwiwa, ta bayyana cewa, kasar Sin za ta kaddamar da wani shiri a tsawon shekaru biyar da nufin taimakawa kamfanoni fiye da 10,000, wajen samun ci gaba mai inganci, tare da hadin gwiwar jami'o'i da kwalejoji sama da 1,000.

Sanarwar ta yi kira da a yi kokarin bullo da sabbin tsare-tsare a kalla guda 30, wadanda aka dorawa alhakin samar da manyan ci gaba a muhimman fannoni, da cibiyoyin bincike na injiniya da dama da masana'antu na kwalejin kirkire-kirkire, bisa la’akari da yadda shirin ya mai da hankali kan bukatun dabarun kasa da batutuwan gama gari da ke damun ci gaban masana'antu.

Sanarwar ta kuma ta zayyana yunkurin da ake da shi, na tallafawa jami'o'i da masana'antu, wajen binciko sabbin dabaru da kirkire-kirkire na hadin gwiwa, da bunkasa tsarin mallakar fasaha bisa bukatu na kasuwa. (Ibrahim Yaya)