logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin ya jaddada bukatar daidaita kasuwanni da samar da ayyukan yi, da zurfafa bude kofa ga waje

2022-07-11 10:24:36 CMG HAUSA

       

   

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya yi kira da a kara kaimi wajen aiwatar da manufofin da suka dace, don daidaita ci gaban kasuwanni da samar da ayyukan yi, da kara bude kofa ga kasashen waje.

Li ya bayyana hakan ne a yayin wani rangadin da ya kai lardin Fujian dake gabashin kasar Sin daga ranar Alhamis zuwa Juma'ar da ta gabata.

Firaminista Li ya saurari rahoto kan yadda ake daidaita ayyukan yi daga gwamnatin lardin, kana ya ziyarci wata unguwar masana’anta mai suna Bosssoft. Da yake yaba nasarorin da unguwannin masana’anta suka cimma wajen samar da masana'antu masu amfani da fasahohin zamani da samar da guraben ayyukan yi da dama kuwa, Li ya bukaci karamar hukumar da ta samar da kudade, don taimaka wa na’urorin rage tsadar kudaden da ake kashewa, kamar kudin haya.

Da yake zantawa da ’yan kasuwa da sabbin daliban da suka kammala karatu a kwalejoji dake aiki a yankin masana’antun, firaminista Li ya ce, ya kamata gwamnati ta karfafa kasuwanci da kirkire-kirkire ta hanyar zaburar da jama’a da dama, musamman matasa su fara kasuwanci da yin kirkire-kirkire.

Li ya saurari wani rahoto kan cinikayyar ketare da zuba jari a lardin Fujian, ya kuma duba tashar jiragen ruwa ta kasa da kasa ta Jinjiang, inda ya bayyana cewa, tashoshin jiragen ruwa, wata babbar hanya ce ta bude kofa ga kasashen waje, da bayar da taimako mai muhimmanci wajen shigowa da fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, inda ya bukaci a zurfafa gyare-gyare a fannin ba da wutar lantarki, da kyautata ka'idoji, da kuma samar da ababen more rayuwa, da inganta yanayin kasuwanci a tashar jiragen ruwa.

Bugu da kari, ya jaddada bukatar aiwatar da tsare-tsaren sassauta dabaru, da ci gaba da saukaka ayyukan kwastam, da kara karfin tashar jiragen ruwa wajen tattarawa da rarrabawa, don ragewa tsadar kudaden da suke kashewa, da daidaita zaton da kasuwa ke da shi, da inganta takarar kasa da kasa. (Ibrahim Yaya)