logo

HAUSA

Cinikin motoci a kasar Sin ya karu zuwa kaso 23.8 a watan Yuni

2022-07-11 20:06:28 CMG Hausa

Kungiyar masu kera motoci ta kasar Sin, ta bayyana a yau Litinin cewa, yanayin sayen motoci a kasar Sin ya kara samun tagomashi a cikin watan Yuni, tana mai alakanta hakan da raguwar barkewar annobar COVID-19 da ingantattun manufofi.

Alkaluman kungiyar sun nuna cewa, an sayar da jimilar motoci miliyan 2.5 a cikin watan Yuni, adadin da ya karu zuwa kaso 23.8 a kan na shekara guda da ta wuce. (Fa’iza Mustapha)