logo

HAUSA

An kaddamar da lambun tsirrai na kudancin kasar Sin

2022-07-11 10:57:40 CMG HAUSA

 


A yau Litinin ne aka kaddamar da lambun killace tsirrai na kasa mafi girma a kudancin kasar Sin. An kaddamar da lambun ne a birnin Guangzhou na lardin Guangdong, wanda shi ne irin sa na 2 bayan wanda yake a birnin Beijing, fadar mulkin kasar.

Lambun na kudancin kasar Sin, shi ne mafi girma a duniya da aka gina a yanki mai dumi, ya kuma kasance cibiyar bincike da kare tsirrai mafi dadewa a kasar Sin.

An tsara fadada girmansa zuwa hekta 319, inda za a rika ba da kariya ga nau’o’in tsirrai daban daban, da nazarin kimiyya, da yayata ilimi a yankunan duniya masu matsakaici da tsananin zafi.

 

A yanzu haka, lambun na da nau’o’in tsirrai da ake baiwa kariya har 17,000, ciki har da nau’o’i 643 da ba su da yawa a duniya, da wadanda ke daf da karewa, da kuma wasu nau’o’in 337 na dazukan kasar Sin da ake killacewa.

Ana kuma sa ran nan da shekaru 3 ko 5 masu zuwa, wannan lambu na tsirrai dake kudancin kasar Sin, zai samar da zarafin ba da kariya ga kaso 95 bisa dari na tsirrai da ba su da yawa a duniya, da wadanda ke daf da karewa a kudancin kasar Sin.  (Saminu Alhassan)