logo

HAUSA

An fitar da sanarwar ranar harkokin teku na kasar Sin ta shekarar 2022 a hukumance

2022-07-11 13:40:16 CMG HAUSA

 

Yau ce “Ranar harkokin teku ta kasar Sin” karo na 18, kana ranar da aka aiwatar da "ranar teku ta duniya" a kasar Sin, an fitar da sanarwar “Ranar harkokin teku ta kasar Sin” ta shekarar 2022 a hukumance. Taken ranar tukin jirgin ruwa ta kasar Sin ta bana shi ne "Jagorancin sabon zamani na rage fitar da hayaki da fasahar zirga-zirgar teku yadda ya kamata".

Ana gudanar da ayyuka daban-daban a fadin kasar don yayata kare muhalli, da rage fitar da iskar carbon, fasaha da ci gaban dorewar zirga-zirgar jiragen ruwa da ma masana'anta.

Kasar Sin babbar kasa ce a fannin teku. Ta kuma zama kasa mafi girman tattalin arziki da girman matakin hadin kan teku da yawan cinikin kayayyaki a duniya.

Kasar Sin ta kuma gina rukunin tashar jiragen ruwa mafi daraja a duniya. Harkokin sufurin ruwa na kasar Sin, ya kai kusan kashi 95 cikin 100 na yawan jigilar kayayyaki na kasa da kasa. Girman jiragen ruwanta, da ingancin ma'aikatan jirgin, da yawan kifayen da take fitarwa ta ruwa, da ma'aunin masana'antu na jiragen ruwa da na'urorin injiniya na ruwa, suna matsayi na farko a duniya. Wannan na nuna cewa kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa a matsayin wata gada da hanyar sadarwa, wajen bunkasa tattalin arzikin duniya da kasuwanci da gina al'umma mai makomar bai daya ga daukacin bil-Adama a duniya. (Ibrahim Yaya)