logo

HAUSA

Kasar Sin na fatan Amurka za ta dauki jerinta da muhimmanci

2022-07-11 20:13:56 CMG Hausa

Yayin ganawar da aka yi baya bayan nan tsakanin ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, da takwaransa na Amurka Antony Blinken, kasar Sin ta gabatar da wasu jerin batutuwa 4 da take fatan jan hankalin Amurkar game da su, ciki har da neman ta gyara kura-kuran da ta tafka game da manufar kasar Sin.

Yayin wani taron manema labarai a yau Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya bayyana wadannan jerin batutuwa a matsayin masu kara jaddada matsayar kasarsa, wadda ke bukatar Amurka ta dakatar da daukar matakan matsin lamba da tsoma baki cikin harkokin gidan Sin da daina raina cikakkaken ikonta da yin katsalandan cikin muradunta na ci gaba da na tsaro.

A cewar kakakin, kasar Sin na fatan Amurka za ta dauki batutuwan da muhimmanci, ta kuma cika alkawarin da shugaban Joe Biden da gwamnatinsa suka dauka ta hanyar nagartattun matakai.

Har ila yau yayin taron manema labaran na yau, Wang Wenbin ya ce kasar Sin na fatan dukkan al’ummar Sri Lanka, za su hada hannu wajen gaggauta shawo kan matsalolin da suke fuskanta da tabbatar da zaman lafiya da farfado da tattalin arzikin kasar tare da kyautata yanayin rayuwarsu. (Fa’iza Mustapha)