logo

HAUSA

Sin ta yi saurin samun karuwar hukumomin kula da hakkin mallakar fasaha

2022-07-11 21:06:22 CMG Hausa

Kasar Sin ta samu saurin karuwar bukatun neman izinin mallakar fasaha da na hukumomin kula da batutuwan mallakar fasaha.

Rahoton raya masana’antar hakkin mallakar fasaha na hukumar kula da mallakar fasaha ta kasar ya nuna cewa, zuwa karshen 2021, akwai hukumomin kula da harkokin neman shaidar mallakar fasaha 3,934 a fadin kasar, wadanda ke da jami’ai masu lasisi 26,840. (Fa’iza Mustapha)