logo

HAUSA

Wang Yi ya gana da takwararsa ta Australia

2022-07-10 15:58:13 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da takwararsa ta kasar Australia Penny Wong, bisa gayyatar da ta yi masa, yayin da yake halartar taron ministocin harkokin wajen rukunin G20, a tsibirin Bali na kasar Indonesiya.

Yayin zantawar ta su, Wang ya bayyana cewa, duk da cewa huldar dake tsakanin Sin da Australia tana fuskantar kalubale, amma ciyar da ita gaba yadda ya kamata, zai dace da moriyar al’ummun kasashen biyu, domin hakan zai taka rawa wajen kiyaye zaman lafiya, da kwanciyar hankali a yankin Asiya da tekun Pasifik.

A cikin ‘yan shekarun da suka gabata, tsohuwar gwamnatin Australia, ta rika mayar da kasar Sin “abokin gaba”, ko “barazana”, amma a yanzu, sabuwar gwamnatin kasar ta nanata cewa, za ta rungumi manufar raya huldar sada zumunta bisa manyan tsare-tsare daga duk fannoni, dake tsakaninta da kasar Sin, da manufar “kasar Sin daya tak a duniya”, yayin da kasar Sin din ke fatan Australia za ta kara fahimtar kasar Sin.

A nata bangare, Penny Wong ta yi tsokaci da cewa, sabuwar gwamnatin kasarta, za ta bi ka’idojin MDD, da dokokin kasa da kasa, da kuma ka’idojin huldar kasa da kasa, kana za ta ci gaba da aiwatar da manufar “kasar Sin daya tak a duniya”, tare kuma da daidaita matsalolin dake gabansu, bisa tushen girmama juna da yin hakuri da juna. (Jamila)