logo

HAUSA

Shugaban kasa da firaministan Sri Lanka na shirin sauka daga mukaman su sakamakon boren gama gari da ya barke a kasar

2022-07-10 16:16:54 CMG Hausa

Shugaban kasar Sri Lanka Gotabaya Rajapaksa, ya amince da yin murabus a ranar Laraba, bayan kazamin bore da al’ummar kasar suka kwashe makwanni suna gudanarwa. Kakakin majalissar dokokin kasar Mahinda Yapa Abeywardena, ya sanar da hakan cikin wata sanarwa ta kafar bidiyo a jiya Asabar. To sai dai kuma kawo yanzu, shugaban kasar bai yi wani jawabi da bakin sa ba.

Shi ma firaministan Sri Lanka Ranil Wickremesinghe, ya ce zai ajiye aikin sa, da zarar dukkanin sassan masu ruwa da tsaki a siyasar kasar sun amince da kafa sabuwar gwamnati. Ofishin firaministan ya ce an kone gidan Mr. Ranil na kashin kan sa, yayin boren da ya rikide zuwa tashin hankali.

Sanarwar yin murabus din manyan jagororin kasar, mai yawan mutane miliyan 22, na zuwa ne bayan da ‘yan kasar suka fita zanga zangar nuna bacin rai game da matsin rayuwa da suke fuskanta.

Masu zanga zanga cikin fushi, sun aukawa ginin fadar shugaban kasa a jiya, bayan da shugaba Rajapaksa ya tsere daga fadar.   (Saminu)