logo

HAUSA

Kungiyoyin Sin da dama sun ba da ra’ayinsu kan hakkin dan Adam a rubuce ga majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD

2022-07-09 16:30:32 CMG Hausa

An gudanar da taron majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD karo na 50 tun daga ranar 13 ga watan Yuni zuwa ranar 8 ga wannan wata a birnin Geneva na kasar Switzerland. Kungiyoyi masu zaman kansu na Sin da dama sun halarci taron tare da ba da ra’ayoyi a rubuce, inda suka bayyana nasarorin da Sin ta samu a fannin kare hakkin dan Adam a dukkan fannoni, da sa kaimi ga yin kwaskwarima da kyautata tsarin kare hakkin dan Adam na duniya.

A cewar kungiyar yin mu’amala da waje ta kananan kabilu ta kasar Sin ta bayyana cewa, a koda yaushe Sin tana nacewa ga manufar kare hakkin dan Adam na mai da jama’a a gaban kome, tana kuma daukar matakan da suka dace, don inganta saurin bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al’ummar jihar Xinjiang, a halin yanzu jama’ar kabilu daban daban suna jin dadin zaman rayuwarsu, da kuma tabbatar kare al’adun gargajiya na kabilun yadda ya kamata. Wasu kasashen yammacin duniya ciki har da kasar Amurka, sun rika yada jita-jita game da jihar Xinjiang, don zubar da kimar Sin da hana bunkasuwarta. Ya kamata majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD ta rika tantance shaidu na hakika, da karya, kuma kada bayanan karya su rika jan hankalinsu.

Cibiyar yin mu’amala a tsakanin kasa da kasa kan batun mata ta birnin Beijing na kasar Sin, ta yi imanin cewa, cutar COVID-19 ta kara tsananta matsalar rashin daidaiton jinsi a duniya. Kungiyoyi masu zaman kansu na kasar Sin, suna baiwa ‘yan mata ilmi da horo, don inganta fasahohinsu, da daukar matakan da suka dace, cimma burin samun daidaito jinsi a fannin kimiyya da fasaha. (Zainab)