logo

HAUSA

Xi Ya Mika Sakon Ta'aziyyar Rasuwar Tsohon Firaministan Japan

2022-07-09 15:49:39 CMG Hausa

Yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon ta'aziyya ga firaministan kasar Japan Fumio Kishida dangane da rasuwar tsohon firaministan kasar ta Japan Shinzo Abe.

A madadin gwamnati da jama'ar kasar Sin, da kuma shi kansa, shugaba Xi ya nuna alhininsa game da rasuwar Abe ba zato ba tsammani, tare da mika sakon ta'aziyya ga iyalan Abe.

Xi ya yi nuni da cewa, a lokacin da yake kan karagar mulki, Abe ya yi kokarin kyautata huldar dake tsakanin kasashen Sin da Japan, kuma ya ba da gudummawa mai kyau ga wannan aiki.

Shugaba Xi ya ce, ya cimma muhimmiyar matsaya tare da Abe game da kulla dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Japan da za ta dace da bukatun sabon zamani, yana mai cewa, ya matukar kaduwa da rasuwar Abe ba zato ba tsammani.

Shugaban na kasar Sin ya ce, a shirye yake ya yi aiki tare da firaminista Kishida, don ci gaba da bunkasa kyakkyawar dangantakar abokantaka da hadin gwiwa tsakanin Sin da Japan bisa ka'idojin da aka kafa a cikin muhimman takardun siyasa guda hudu tsakanin kasashen biyu.(Ibrahim)