logo

HAUSA

Ayyukan da Sin ke ba da gudummowar aiwatarwa a Kongo Brazzaville na taka muhimmiyar rawa wajen hadin gwiwar kasashen biyu a fannonin al'adu da kiwon lafiya

2022-07-08 10:54:09 CMG Hausa

A watan Maris din shekarar 2013, yayin ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai Jamhuriyar Kongo, ya halarci bikin kaddamar da dakin karatu na jami'ar Marien Ngouabi, tare da yanke kyalle don murnar kammala aikin gina asibitin sada zumunci tsakanin Sin da Kongo Brazaville.

Jami'ar Marien Ngouabi da ke Brazzaville, babban birnin kasar Kongo Brazzaville, ita ce jami'ar gwamnati mafi girma a kasar, kuma dakin karatu na jami'ar da aka gina karkashin taimakon kasar Sin, shi ne mafi fadi, wanda kuma ke da na’urorin zamani mafi yawa a kasar.

Asibitin sada zumunta na Sin da Kongo Brazaville, wanda aka gina shi bisa taimakon kasar Sin, ya taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannin kiwon lafiya a 'yan shekarun nan.

A cewar shugaban asibitin Benjamin Ngakono, asibitin ya zama daya daga cikin manyan asibitoci mafiya girma a kasar, kuma daya daga cikin muhimman asibitocin dake kula da masu fama da cutar COVID-19.

“A cikin shekaru kusan goma da suka gabata, asibitin sada zumunci na Sin da Kongo Brazaville, yana gudanar da ayyukansa yadda ya kamata, yana ba da hidimar jinya ga mazauna yankin Mfilou. Kamar yadda kuke gani, mazauna wurin suna matukar martaba ayyukan jinya na asibitin." (Mai fassara: Bilkisu Xin)