logo

HAUSA

Kasashen Sin da Rasha sun yi alkawarin fadada hadin gwiwa da kare muradun kasashe masu tasowa

2022-07-08 11:49:35 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi da takwaransa na Rasha, Sergei Lavrov, sun amince da fadada dangantakar kasashensu, tare da hada hannu wajen kare muradun bai daya na kasashe masu tasowa.

Yayin ganawarsu a gefen taron kungiyar kasashen G20 a birnin Bali na Indonesia, Wang Yi ya ce karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu, Sin da Rasha sun ci gaba da tuntubar juna da ingiza hadin gwiwa a fannoni daban-daban, lamarin da ya nuna juriya da kudurinsu na hadin gwiwa.

A nasa bangaren, Sergei Larov ya ce, Rasha da Sin sun taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye ka’idojin MDD da dokokin kasa da kasa da inganta odar duniya da ingiza dangantakar demokradiyya tsakanin kasa da kasa ta hanyar daukar matsayar da ta kamata da kiyaye hadin gwiwarsu, wadanda kasashe masu tasowa suka amincewa tare da goya musu baya.

Bangarorin biyu sun kuma tattauna kan yanayin Ukraine, inda ministan na Rasha ya bayyana yanayin da kasarsa da Ukraine ke ciki da kuma matsaya da kudurinta kan batun.

Har ila yau, Wang Yi ya ce Sin za ta ci gaba da daukar matsayar da ta dace cikin adalci, da mayar da hankali kan lafawar yanayin da inganta tattaunawar zaman lafiya da mara baya ga dukkan yunkurin da zai kai ga warware matsalar cikin lumana.

Bugu da kari, bangarorin biyu sun amince da taimakawa Indonesia cimma nasarar karbar bakuncin taron ministocin harkokin wajen G20 tare da karfafa hadin gwiwa karkashin tsarin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai. (Fa’iza Mustapha)