logo

HAUSA

Darajar jimilar cinikayyar duniya ta kai dala triliyan 7.7 a rubu’in farko na bana

2022-07-08 16:24:59 CMG Hausa

A ranar Alhamis, taron karawa juna sani na cinikayya da samar da ci gaba na MDD, ya fitar da rahoton dake cewa, darajar jimilar cinikayyar duniya ta kai dalar Amurka triliyan 7.7 a rubu’in farko na shekarar bana, adadin da ya karu da dalar triliyan 1, bisa na rubu’in farko na shekarar 2021, kuma karuwar cinikayyar yankuna daban daban tana cikin matsayi mai karfi.

Taron ya kuma yi hasashen cewa, ko da yake cinikayyar duniya za ta ci gaba da karuwa, amma saurin karuwar cinikayyar zai ci gaba da raguwa a rubu’i na biyu, kuma hauhawar farashin kayayyaki da rikicin Rasha da Ukraine ya haddasa, zai yi tasiri ga cinikayyar duniya, da habakar kudin ruwa na bankuna, yayin da dabarun karfafa tattalin arziki a hankali, na iya yin mummunan tasiri ga kasuwancin duniya.(Safiyah Ma)