logo

HAUSA

UNDP: Tsadar rayuwa ta jefa mutane miliyan 71 cikin kangin talauci

2022-07-08 10:47:25 CMG Hausa

Wani rahoto da shirin samar da ci gaba na MDD, ko UNDP ya fitar a jiya Alhamis, ya nuna yadda tsadar rayuwa ta jefa kimanin mutane miliyan 71 cikin kangin talauci a kasashe masu tasowa, tun daga watan Maris na shekarar nan ta 2022.

Rahoton ya ce akwai yiwuwar a fuskanci karin hauhawar farashin kayayyaki, da karuwar kudin ruwa, wadanda za su kara jefa mutane cikin yanayin komadar tattalin arziki, wanda ke zurfafa halin fatara da al’ummun duniya ke fuskanta a sassan duniya baki daya.

Alkaluman kiyasi na binciken da aka gudanar a kasashe masu tasowa na duniya 159, sun nuna yadda farashin muhimman kayayyakin amfanin yau da kullum suka yi tashin gwauron zabi, yanayin da ke haifar da matukar matsi ga iyalai matalauta, musamman mazauna kasashen yankin Balkan, da kasashen dake kewayen tekun Caspia, da na yankin Sahel ta Afirka. (Saminu Hassan)