logo

HAUSA

Sin tana fatan kasar Amurka za ta canja manufofinta kan kasar Sin

2022-07-08 20:37:11 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya jaddada a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, Sin tana fatan kasar Amurka za ta saurari ra’ayoyi da canja manufofinta bisa manyan tsare-tsare game da kasar Sin, ta kuma yi zabin da ya dace.

A kwanakin baya ne, shugaban kamfanin STARR na kasar Amurka kuma mataimakin shugaban gudanarwar kwamitin kula da dangantakar dake tsakanin Amurka da Sin na kasar Amurka Maurice R.Greenberg ya wallafa wani sharhi a jaridar The Wall Street mai taken “Muna fatan kyautata dangantakar dake tsakaninmu da Sin”, inda ya bayyana cewa, dangantakar dake tsakanin Amurka da Sin, dangantaka ce mafi muhimmanci a duniya. A halin yanzu fiye da kowa ne lokaci, kyautata dangantakar ya fi dace da moriyar kasar Amurka.

Zhao Lijian ya amince da ra’ayin Mr. R.Greenberg kan dangantakar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka, yana mai bayyana cewa, a cikin shekaru fiye da 10 da aka raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, ya nuna cewa, hadin gwiwa da samun moriyar juna shi ne kadai zabin da ya dace wajen raya dangantakarsu, kuma hakan zai amfanawa jama’ar kasashen biyu har ma ga duniya baki daya. Sin tana fatan kasar Amurka za ta hada kai tare da kasar Sin, da kyautata dangantakar dake tsakaninsu bisa ka’idojin girmama juna da zama tare cikin lumana da kuma hadin gwiwa da samun moriyar juna, don dawo da dangantakarsu yadda ya kamata. (Zainab)