logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Yi Kira Da A Nace Kan Ra'ayin Hadin Gwiwa Na Hakika A Taron G20 A Indonesia

2022-07-08 20:28:16 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi kira a yau Juma'a ga kasashen duniya a tsibirin Bali na kasar Indonesia, da su tsaya tsayin daka kan hadin gwiwa tsakanin bangarori daban-daban, da raya hulda mai inganci a wannan lokaci mai cike da kalubaloli.

Wang ya bayyana hakan ne a yayin taron ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar G20 da aka gudanar a tsibirin Bali na kasar Indonesia.

Wang Yi ya ce, da farko, ya kamata kasashe su kasance abokan hulda tare da mutunta juna da tuntubar juna bisa daidaito. Kamata ya yi a tafiyar da harkokin kasa da kasa ta hanyar tuntubar juna tsakanin kasashe, kana a kiyaye dokokin kasa da kasa cikin hadin gwiwa.

Na biyu, ya kamata kasashe su kasance abokan zaman tare cikin lumana da hadin gwiwar moriyar juna. Yana mai cewa, sai wata kasa ta mutunta tsaron wasu kuma ta kiyaye tsaron kowa ne, kafin ta iya samun nata tsaro na hakika. Wang ya kara da cewa, yadda wata kasa ta fifita tsaronta a kan tsaron sauran kasashe da kuma karfafa kawancen soji, na iya haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin kasashen duniya, da kuma sanya kanta cikin rashin kwanciyar hankali.

Kana na uku, ya kamata kasashe su kasance abokan hadin gwiwa ba tare da wata rufa-rufa ba, da damawa da kowa, da yin cudanya da juna. Wang ya ce, ya kamata takara tsakanin kasa da kasa ta kasance mai adalci, kuma bai kamata ta zama mummunar gasa ba ko ma yin fito na fito da juna.(Ibrahim)