logo

HAUSA

Rasha: Jinkirin tattaunawa yana kara mayar da hannun agogo baya

2022-07-08 10:05:31 CMG Hausa

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ce, kasarsa a shirye take ta ci gaba da tattaunawar shulhu da kasar Ukraine, sai dai kuma tsaikon da ake samu na kara mayar da hannun agogo baya.

Shugaba Vladimir Putin, wanda ya bayyana hakan a jiya Alhamis, yayin wani taro tare da manyan jami’an fadar mulki, da shugabannin jam’iyya mai mulki, a zauren majalissar dokokin kasar ta Duma. Ya ce, masu jan kafa game da tattaunawa su sani cewa, jinkirin da ake fuskanta a yanzu, na kara nisanta yiwuwar cimma matsaya da Rasha.

Mr. Putin ya kara da cewa, cikin tsawon lokaci, kasashen yammacin duniya na matukar muzgunawa Rasha. Kaza lika sun yi watsi da shawarar Rasha ta samar da wani tsarin tsaro na bai daya, wanda zai baiwa nahiyar Turai kariya. Sun kuma ki amincewa da manufar hadin gwiwa, ta magance batun tsaron makamai masu linzami. Yayin da kuma suka yi fatali da kashedin Rasha na dakatar da fadada ikon NATO.

Daga nan sai shugaban na Rasha ya sha alwashin ganin bayan yunkurin na kasashen yamma, yana mai cewa kokarinsu na kakabawa duniya wani sabon tsarin mallaka ba zai yi nasara ba. (Saminu Hassan)