logo

HAUSA

Shugaba Buhari ya nuna bacin ransa game da gazawar tsarin tattara bayanan sirri a gidajen yarin Najeriya

2022-07-07 11:38:25 CMG Hausa

Jiya Laraba, shugaban tarayyar Nijeriya Muhammadu Buhari, ya kai ziyara gidan yarin Kuje dake birnin Abuja, inda ya nuna bacin ransa game da gazawar tsarin tattara bayanan sirri a gidajen yarin Najeriya, da ma yadda ake amfani da tsarin.

Cikin wata sanarwar da ya fitar a jiya Laraba, babban sifeton gidajen gyaran hali na Najeriya Abubakar Umar ya ce, gaba daya, akwai fursunoni 994 a gidan yarin na Kuje, kuma maharan da suka aukawa gidan sun saki fursunoni 879, amma an sake kama fursunoni sama da dari 4 daga cikinsu.

A halin yanzu kuma, akwai fursunoni 443 da suka tsere, cikin har da ’yan Boko Haram 63 dake cikin gidan yarin.

Rahotanni sun tabbatar da rasuwar mutane 5 sakamakon wannan hari, yayin da wasu 19 suka jikkata. (Maryam)