logo

HAUSA

Adadin motoci masu amfani da sabon makamashi ya zarta miliyan 10 a Sin

2022-07-07 10:00:38 CMG Hausa

Rahoton ma’aikatar tabbatar da kwanciyar hankalin jama’a ta kasar Sin ya nuna cewa, ya zuwa karshen watan Yunin bana, jimillar adadin motocin kasar ya kai miliyan 406, inda daga cikinsu, motocin dake amfani da sabon makamashi mai inganci suka kai fiye da miliyan 10.01.

Kaza lika adadin sabbin motocin dake amfani da sabon makamashi da aka yi rajista a cikin watanni shida, na farkon shekarar bana a fadin kasar, ya kai miliyan 2 da dubu 209, adadin da ya karu da miliyan 1 da dubu 106, bisa na makamancin lokacin bara, wato ya karu da kaso 100.26 bisa dari, wanda kuma ya kai matsayin koli a tarihi.

An lura cewa, adadin motocin dake amfani da sabon makamashi mai inganci da aka yi rajista a bana, ya kai kaso 19.90 bisa dari, cikin daukacin motocin da aka yi rajistar su a shekarar. (Jamila)