logo

HAUSA

Gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da yin gyaran fuska ga ayyukan aiwatar da kasafin kudi da sauran ayyuka masu nasaba da hakan

2022-07-07 14:08:28 CMG Hausa

Taron majalissar zartaswar kasar Sin, ya tsara dabarun ci gaba da gudanar da gyare gyare bisa matsalolin da ake ganowa, yayin da ake aiwatar da kasafin kudi, ta hanyar bincikar tsarin aiwatar da kasafin, da sauran sassa masu nasaba, wadanda suka hada da tattara haraji da kashe kudade.

Yayin taron na jiya Laraba, wanda firaministan kasar Li Keqiang ya jagoranta, an amince da fadada amfani da lasisi na zamani, da sauran takardun shaidar hada hadar kudade bisa tsari, domin kara kyautata kuzarin sassan kasuwanni.   (Saminu)