logo

HAUSA

Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta yabawa China Daily saboda bincike tare da gabatar da bayanai game da jita-jitar da wata hukumar Birtaniya ta bayar kan batun Xinjiang

2022-07-07 20:37:11 CMG Hausa

Yayin taron manema labarai da aka yi yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya yabawa kafar watsa labarai ta kasar Sin wato China Daily, bisa yadda ta yi bincike tare da gabatar da bayanai game da jita-jitar da wata hukumar ilmi ta kasar Birtaniya ta bayar kan jihar Xinjiang, inda ya jaddada cewa, ko da yake an shirya jita-jitar kamar gaskiya, ba wani abu ba ne face zargi mara tushe.

Rahotanni na cewa, tun daga watan Mayun shekarar 2021, cibiyar Helena Kennedy ta jami’ar Sheffield Hallam ta Birtaniya, ta gabatar da rahotanni 4 a jere kan jihar Xinjiang, wadanda suka yada karairayi na aikin tilas a jihar. Sai dai a kwanakin baya, jaridar China Daily ta yi bincike kan rahotannin, inda ta gano cewa akwai wata kungiyar da ta bayar da irin jita-jitar, kana masu rubuta rahotannin da masu zuba jari ga cibiyar, suna da nasaba da kungiyar ta’addanci.

Zhao Lijian ya ce, an tabbatar da cewa, wasu abubuwan da aka bayyana cikin rahotannin labarai ne marasa tushe, wasu kuma jita-jita ne da cibiyar nazarin manufofi ta kasar Australia ta bayar. Ya ce masana masu gabatar da rahotannin sun lalata ilminsu ta hanyar bayar da jita-jita game da aikin tilas a jihar Xinjiang, kana sun samu kudi daga Amurka tare da taimaka mata wajen yada jita-jita. (Zainab)