logo

HAUSA

Za a gudanar da bikin baje kolin littattafai na Hongkong karo na 32

2022-07-07 16:27:51 CMG Hausa

A ranar 6 ga watan Yuli, kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya labarta cewa, a ranar hukumar bunkasuwar cinikayyar Hongkong ta gudanar da taron ’yan jarida, inda ta sanar da cewa, za a gudanar da bikin baje kolin littattafai na Hongkong karo na 32, daga ranar 20 zuwa 26 ga watan Yuli a cibiyar baje koli ta Hongkong, inda za a gudanar da lakcoci, da ayyukan al’adu fiye da 600.

Bisa bayanin da aka yi, jigon bikin baje kolin littattafan na bana, shi ne “Al’adu da tarihi, da birni ya rubuta su”.

Yayin taron ’yan jarida, mataimakin shugaban hukumar bunkasuwar cinikayyar Hongkong, Zhang Shufen ta bayyana cewa, bikin baje kolin littattafai na wannan karo yana da muhimmancin musamman. Ya ce Hongkong ya bunkasa daga wani karamin kauyen kamun kifi zuwa wani babban birni na duniya, kuma littattafai da kalmomi masu kyau da yawa sun nadi abubuwa dake faruwa yayin bunkasuwar yankin, wadannan littattafai za su jagoranci masu karanta su da su yi tafiya kamar a kan wata hanyar tarihi, da al’adu, da kuma jin dadin sawun birnin Hongkong. (Safiyah Ma)