logo

HAUSA

Amurka ce kan gaba wajen amfani da sararin samaniya a matsayin makami kuma fagen daga

2022-07-07 20:20:47 CMG Hausa

 

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, ya mayar da martani ga tsokacin da hukumar kula da sararin samaniya ta Amurka wato NASA ta yi, dangane da shirye-shiryen Sin da suka shafi sararin samaniya, inda ya ce, ya kamata Amurka ta daina watsi da gaskiya tana kokarin bata sunan kasar Sin. Haka kuma, ya kamata ta nazarci kalamai da ayyukan da ba su dace ba da take aiwatarwa a sararin samaniya, kana ta sauke nauyin dake wuyanta a matsayinta na babbar kasa. Har ila yau, ya yi kira ga Amurka ta kara kokarin bayar da gudunmuwa ga kyautata dangantakarta da Sin a fannin ayyukan da suka shafi sararin samaniya.

Zhao Lijian, ya ce Amurka ce babbar mai amfani da sararin samaniya a matsayin makami kuma fagen daga. Ya ce ta dade tana aiwatar da manufofin da suka shafi sararin samaniya, kamar samarwa da harba makamai da kuma gudanar da atisayen soji akai akai.

A cewar kakakin, kasar Sin na kiyaye amfani da sararin samaniyar ta hanyar lumana, haka zalika tana neman hadin gwiwa da kasa da kasa a bangaren. Ya ce tun bayan kaddamar da shirinta na kafa cibiyar bincike a sararin samaniya, Sin ke nacewa ga ka’idojin aiwatar da shirin cikin lumana, daidaito da moriyar juna da neman ci gaba na bai daya, haka kuma ta rattaba hannu kan yarjejeniyoyi da hukumomi da kungiyoyin kula da sararin samaniya na kasa da kasa, wadanda suka samar da kyawawan sakamako. (Fa’iza Mustapha)