logo

HAUSA

Firaministan Burtaniya ya yi murabus

2022-07-07 20:34:51 CMG Hausa

 

Boris Johnson ya yi murabus daga mukaminsa na firaministan kasar Birtaniya kuma shugaban jam’iyyar Conservative.

Yayin jawabinsa ga kasar a yau Alhamis, Boris Johnson ya ce zai ci gaba da aikin firaminista har zuwa lokacin da aka zabi sabon shugaban jam’iyyar. (Fa’iza Mustapha)