logo

HAUSA

A kalla fursunoni 300 ne suka tsere bayan harin da ‘yan bindiga suka kai gidan yarin Najeriya

2022-07-06 20:40:53 CMG Hausa

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa, a kalla fursunoni 300 ne suka tsere, bayan da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, sun kai hari a wani gidan yari da ke Abuja, babban birnin kasar.

Babban sakatare a ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar Shu’aibu Belgore, ya shaidawa manema labarai yayin ziyarar da ya kai gidan yarin Larabar nan cewa, maharan sun kai hari kan gidan yarin Kuje dake Abuja ne jiya da dare, inda suka saki fursunoni kusan 600, amma an sake kama rabin wannan adadi. (Ibrahim)