logo

HAUSA

Kasar Sin za ta gina biranen gwaji masu amfani da na’urori masu kwakwalwa

2022-07-06 15:29:24 CMG Hausa

A ranar 5 ga wata, shugaban sashen kula da kasuwar gine-gine na ma'aikatar gidaje da raya birane da kauyuka na kasar Sin, ya ce ma'aikatar tana zabar wasu birane inda za a sanya su zama birane masu yin amfani da fasahohi masu kwakwalwa, matakin da ake fatan zai taka muhimmiyar rawa wajen inganta sauye-sauye, da ci gaba mai inganci a fannin masana'antar gine-gine.

Wannan shugaba ya ce, an tsara ayyuka hudu da dole ne a yi lokacin da ake tsara shirye-shiryen gwaji, wato kyautata tsarin manufofi, da bunkasa masana’antar gine-gine masu amfani da fasahohi masu kwakwalwa, da gudanar da ayyukan nune-nunen gwaji, da kuma samar da tsarin gudanarwa.

Sannan za a mai da hankali kan gina wasu sansanonin masana’antu masu amfani da fasahohi masu kwakwalwa, da bunkasa sabbin masana’antu masu nasaba da amfani da fasahohi masu kwakwalwa a bangaren kirar lamba, da sarrafawa, da kere-kere, da gine-gine, da gudanarwa, da amfani da mutum-mutumin gini, da yanar gizo a masana'antun zamani. Bugu da kari, za a gina yankunan irin wadannan masana’antu masu amfani da fasahohi masu kwakwalwa wajen gina gidaje.

Bugu da kari, shugaban ya ce, biranen gwajin za su iya samar da sabbin ayyuka bisa makasudin gwaji. (Safiyah Ma)