logo

HAUSA

Masanan kasa da kasa sun amince da sakamakon Sin a fannin kare hakkin bil adam

2022-07-06 10:50:01 CMG Hausa

A jiya Talata ne aka kira taro mai taken “Kara karfafa aikin gudanar da harkokin hakkin dan adama, domin kare hakkin bil adama yadda ya kamata” na hukumar kare hakkin dan adam ta MDD karo na 50 ta kafar bidiyo, inda masana mahalartan taron suka yi tattaunawa mai zurfi kan batun, da yadda za a tafiyar da harkokin kare hakkin dan adam a fadin duniya.

Yayin taron, malamin ilmin siyasa na jami’ar Buea ta kasar Kamaru Hassan Njoya, ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, kasashe masu tasowa suna fuskantar kalubale a fannoni guda biyu, yayin da suke kokarin kare hakkin dan adam, wato kasashe masu nuna fin karfi suna tsoma baki a cikin harkokin gidan sauran kasashe, haka kuma suna tilastawa kasashe masu tasowa, amince da manufofi irin na kasashen yamma, yana mai cewa,

“Ya dace a girmama bambancin al’adu, da tsarin siyasa na kasa da kasa, kuma a ko da yaushe kamata ya yi a daidaita rikici ta hanyar tattaunawa, kana dole ne a yi kokari domin ingiza adalci tsakanin kasa da kasa a fannonin siyasa da tattalin arziki da sauransu.”

Malamin nazarin ilmin zamantakewar al’umma na jamilar Cork ta kasar Ireland Feilim Hadhmail, shi ma ya yi tsokaci da cewa, kasar Sin tana taka rawa ta musamman, wajen ingiza zaman lafiya, da kare hakkin dan adam a fadin duniya, a cewarsa:

“Kasar Sin, babbar kasa ce dake taka rawa matuka a fadin duniya, a kasar ta Sin, al’ummomi suna da yawa, kuma tattalin arzikin kasar ya samu ci gaba cikin sauri, kana kasar tana samar da goyon baya ga kasashe masu tasowa yayin da suke raya tattalin arziki, kaza lika Sin ta samu amincewa daga yawancin kasashen duniya, a bangarorin ingiza zaman lafiya, da tattaunawa tsakanin kasa da kasa. Ana iya cewa, kasar Sin ta kasance wata gada, yayin da ake tafiyar da harkokin kasa da kasa.” (Jamila)