logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen Sin zai gana da takwaransa na Amurka

2022-07-06 10:47:33 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen Sin kuma mamban majalisar gudanarwar kasar, Wang Yi, zai tattauna da ministocin harkokin wajen manyan kasashe da wakilan kungiyoyin shiyyoyi, a gefen taron ministocin harkokin wajen G20.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, ya kuma bayyana cewa, bisa amincewar kasar Sin da Amurka, Wang Yi zai gana da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a gefen taron na G20, inda za su tattauna game da dangantakar kasashensu da muhimman batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya. (Fa’iza Mustapha)