logo

HAUSA

Nijeriya za ta kaddamar da jirgin samanta a karshen bana

2022-07-06 13:23:25 CMG Hausa

Ministan kula da sufurin jiragen sama na Nijeriya Hadi Sirika, ya ce gwamnati ta bada lasisin sufurin jiragin sama, inda zata kaddamar da sabon jirginta a karshen bana.

Hadi Sirika ya bayyana haka ne yayin wani taron yini biyu na hadin gwiwar zuba jari tsakanin gwamnati da bangarori masu zaman kansu, jiya a Abuja.

Ministan ya bayyana cikin watan Nuwamban da ya gabata cewa, wani kamfani ne zai tafiyar da harkokin jirgin saman, inda gwamnatin Nijeriya zata mallaki kaso 5 na hannun jari, kana ‘yan kasuwar kasar za su dauki kaso 46, yayin da aka kebe ragowar kaso 49 ga wasu muhimman abokan hulda da ba a kai ga tabbatar da su ba, cikinsu har da masu zuba jari daga ketare.

Jirgin Air Nigeria ya tsayar da aiki ne a watan Satumban 2012, saboda kalubalen kudi da na gudanarwa. (Fa’iza Mustapha)