logo

HAUSA

Hana Wani Hana Kai

2022-07-06 20:34:57 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, wanda ya kawo cikas ga wasu kasashe a fannin raya fasahohi sannan yake ba da kariya ga fasahohi yana kawo wa kansa cikas ne.

Rahotanni na cewa, kasar Amurka tana kokarin matsawa kasar Netherlands lamba da ta hana kamfanin ASML na kasar sayar wa kasar Sin kananan na’urorin laturoini da sauran muhimman fasahohi, amma gwamnatin kasar Netherlands ba ta yarda ba tukuna.

Game da wannan batu, Zhao Lijian ya yi nuni da cewa, wannan wani misali ne na yadda kasar Amurka take yin amfani da karfinta da kuma dogaro kan fasahohi don tilastawa sauran kasashe, su bi manufar kama karya ta kasar Amurka a fannin fasahohi, kuma wannan ta’addaci ne a fannin raya fasahohi.

Zhao Lijian yana fatan bangarori daban daban da abin ya shafa, za su tsaya tsayin daka, da ci gaba bin ka’idojin samun moriya na dogon lokaci da kasuwanci cikin gaskiya da adalci, da kuma yanke shawara cikin ‘yanci. (Zainab)