logo

HAUSA

Jagoran faladinu da na Hamas sun gana a Aljeriya

2022-07-06 13:32:03 CMG Hausa

 A jiya Talata ne shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas, ya gana da shugaban kungiyar Hamas Ismail Haniyeh a kasar Aljeriya. Fadar gwamnatin Falasdinawa, ta ce shugaban kasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune, ya halarci tattaunawar da jagororin biyu suka gudanar.

An watsa tattaunawar ta kafar talabijin na TV3 dake Aljeriya, daga karshe an kuma ga shugabannin 3 na rike da hannuwan juna.

Abbas da Haniyeh, sun isa kasar Aljeriya, albarkacin bikin cikar kasar shekaru 60 da samun ‘yancin kai daga Turawan kasar Faransa.  (Saminu)