logo

HAUSA

An kira taron dandalin manyan kafofin watsa labarai a Beijing

2022-07-05 10:23:17 CMG Hausa

A jiya Litinin ne aka kaddmar da taron dandalin manyan kafofin watsa labarai, mai taken “Ci gaban duniya: Nauyin dake wuya, da matakan da za a dauka”, a birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin, inda mamban hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, kuma ministan ma’aikatar yada manufofin kasar Huang Kunming ya halarci bikin kaddamar da taron, tare da karanta sakon taya murna na shugaban kasar Xi Jinping, da kuma gabatar da wani muhimmin jawabi.

A cikin jawabinsa, Huang Kunming ya yi nuni da cewa, sakon Xi ya yi cikakken bayani kan yanayi, da kalubale da daukacin kasashen duniya ke fuskanta, yayin da suke kokarin ingiza ci gaban duniya, ya kuma sanar da manufar kasar Sin ta tabbatar da shawarar ci gaban duniya, domin ciyar da dukkanin duniya gaba yadda ya kamata.

Huang Kunming ya jaddada cewa, shawarar ci gaban duniya wadda shugaba Xi ya gabatar ta samu amicewa daga al’ummomin kasa da kasa, kana ta taka babbar rawa wajen ingiza ajandar dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030 ta MDD, da kuma hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa. Ya ce kasar Sin tana fatan yin kokari tare da sauran kasashen duniya, domin cimma burin samun wadata tare. (Jamila)