logo

HAUSA

Sakamakon taron BRICS a wasu muhimman bangarori 8 za su amfanawa Afrika ta kudu

2022-07-05 14:28:43 CMG Hausa

Jakadan kasar Sin a Afrika ta kudu Chen Xiaodong, ya ce muhimman bangarori 8 daga cikin dimbin sakamakon taron kolin kungiyar BRICS karo na 14 da aka kammala a baya bayan nan, za su amfanawa Afrika ta kudu da ma nahiyar Afrika baki daya.

Wani sharhi na Chen Xiaodong, da aka wallafa a shafin website na babbar kafar yada labarai ta Afrika ta kudu wato Independent Online, a ranar 29 ga watan Yuni, ya ruwaito jakadan na cewa, an kaddamar da cibiyar bincike da samar da allurar riga kafi ta kungiyar BRICS, inda za ta kasance wani dandalin hadin gwiwa kan bincike da samar da allurar riga kafi ga kasashe masu tasowa, lamarin da zai kai ga cike gibin da ake fama da shi na karancin alluran riga kafi.

A bangaren wadatar abinci kuwa, a karon farko, kasashen BRICS sun hada gwiwa wajen samar da wata dabara da kafa wani dandali kan raya karkara da ayyukan gona.

A cewar jakadan, kasashen BRICS sun cimma hadin gwiwa kan wani tsarin raya tattalin arzikin bangaren intanet tare da gabatar da wani shirin sauye sauyen fasahohin zamani a bangaren sarrafa kayayyaki

Haka kuma, taron ya lalubo sabbin damarmakin raya fasahohi da inganta su, tare da samar da wata cibiyar kimiyya da fasaha, domin shawo kan tarin barazana da kalubalen da duniya ke fuskanta.

A cewarsa, kasashen na BRICS sun yi kokari ta hanyoyi daban-daban, wajen habaka farfadowa da bunkasa tattalin arzikin duniya.

Chen Xiaodong ya kara da cewa, kasashen BRICS sun kuma kaddamar da wani sabon shiri na yaki da cin hanci, wanda a karkashinsa, za su inganta karfinsu na hadin gwiwa.

Sakamako na 7 shi ne, kirkiro sabuwar hanyar horar da jami’ai. Sai kuma na 8 a cewarsa shi ne, gabatar da sabbin shawarwarin kyautata tsarin shugabanci a duniya. (Fa’iza Mustapha)