logo

HAUSA

Mutane 6 aka kashe yayin wani harin bindiga da aka kai jihar Illinois

2022-07-05 10:20:10 CMG Hausa

Mutane 6 ne aka tabbatar sun mutu, yayin wani harin bindiga da aka kai a lokacin faretin ranar ‘yancin kai, da safiyar jiya Litinin, a yankin Highland Park dake arewacin birnin Chicago na jihar Illinois ta Amurka.

Baya ga mamatan, akwai wasu 31 da suka jikkata da aka garzaya da su asibiti, inda 12 daga cikinsu ke cikin yanayi mai tsanani. An bayyana maharin a matsayin namiji, farar fata, mai shekaru tsakanin 18-20

Wata sanarwa da aka wallafa a shafin website na yankin Highland Park, ta shawarci mutane su kauracewa tsakiyar yankin, tana mai cewa har yanzu maharin bai shiga hannu ba.

An samu bindiga a wajen da aka kai harin. Haka kuma, jami’an tsaro na farautar maharin.

Yankin Highland Park, muhimmin wuri ne dake da nisan kilomita 43 daga arewacin Chicago. (Fa’iza Mustapha)