logo

HAUSA

An kama wanda ake zargi da kai harin bindiga a jihar Illinois ta Amurka

2022-07-05 11:44:13 CMG Hausa

‘Yan sanda sun tabbatar da cafke wanda ake zargi da kai harin bindiga, yayin faretin ranar samun ‘yancin kai, a yankin Highland Park dake birnin Chicago, na jihar Illinois ta Amurka.

Yayin wani taron manema labarai, ‘yan sandan sun ce sun kama Robert Bobby Crimo III, mai shekaru 22, ba tare da wata turjiya ba.   

Mutane 6 ne aka tabbatar sun mutu, yayin harin na safiyar jiya Litinin. Baya ga mamatan, akwai wasu 31 da suka jikkata da aka garzaya da su asibiti, inda 12 daga cikinsu ke cikin yanayi mai tsanani.

Tun da farko kafin a kama maharin, an wallafa wata sanarwa a shafin website na yankin Highland Park, inda aka shawarci jama’a su kauracewa tsakiyar yankin.

Yankin Highland Park, muhimmin wuri ne dake da nisan kilomita 43 daga arewacin Chicago. (Fa’iza Mustapha)