logo

HAUSA

An fitar da rahoton nazari game da yanayin aiki na al’ummun yankin Xinjiang

2022-07-04 13:45:24 CMG Hausa

An wallafa rahoton nazari mai taken “Bayani kan hakikanin yanayin aiki na al’ummu ‘yan kabilu daban daban na yankin Xinjiang” a shafin yanar gizo na jami’ar Xinjiang a yau Litinin da safe. Rahoton ya bayyana hakikanin yanayin aiki na al’ummun, bayan gudanar da bincike a sassan dake fadin yankin.

Masanan kungiyar nazarin da ta fitar da rahoton sun shafe shekara guda suna bincike mai zurfi a unguwanni da kauyuka na gundumomi da birane da yawansu ya kai 14 dake fadin yankin Xinjiang, inda suka tattauna da ma’aikatan yankin ‘yan kabilun Han da Uygur da Kazak da Hui da Xibe da Dongxiang da Daur da Rasha da sauransu, domin kara fahimtar makasudi da hanyoyin gudanar da ayyukansu.

Rahoton ya bayyana cewa, al’ummun yankin Xinjiang na kasar Sin suna gudanar da aiki ne bisa bukatunsu, kuma yanayin aikin da suke ciki ya dace da ci gaban zamantakewar al’umma, kana al’ummun yankin sun cimma burinsu na jin dadin rayuwa ta hanyar gudanar da aikin da suka zaba. (Jamila)