logo

HAUSA

Shugaban Zimbabwe ya gana da babban jami’in diplomasiyyar Sin

2022-07-04 10:04:17 CMG Hausa

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya gana da Yang Jiechi, babban jami’in diplomasiyyar kasar Sin, inda suka yi alkawarin daukaka musaya da hadin gwiwa da muhimmiyar dangantakar dake tsakanin kasashensu zuwa wani sabon mataki.

Yayin ganawar da aka yi jiya Lahadi a Harare, babban birnin Zimbabwe, Yang Jiechi, wanda mamba ne na ofishin harkokin siyasa kuma daraktan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin kolin JKS ya mikawa shugaban na Zimbabwe sakon gaisuwa daga shugaba Xi Jinping.

A cewarsa, rashin kwanciyar hankali da rashin tabbas da rashin tsaro su ne muhimman matsalolin da duniya ke fuskanta. Kuma a baya-bayan nan, kasar Sin ta shirya taron tattaunawa ta manyan jami’ai game da ci gaban duniya karkashin tsarin BRICS Plus, wanda ya aike da sako mai karfi na kasashe masu tasowa, na inganta ci gaba da hadin gwiwar duniya. Ya kara da cewa, a shirye kasar Sin take ta hada gwiwa da Zimbabwe, wajen daukaka tsarin kasa da kasa karkashin MDD da kiyaye dokokin kasa da kasa tare da tabbatar da tsarin shugabancin duniya bisa gaskiya da adalci.

A nasa bangare, shugaba Mnangagwa ya ce abota tsakanin Zimbabwe da Sin ta kara karfi. Kuma Zimbabwe na goyon bayan kokarin kasar Sin na kare cikakken ‘yancinta, da adawa da tsoma baki daga waje da kakaba takunkumai, haka kuma ya godewa kasar Sin bisa taimakon da ta shafe shekaru tana ba Zimbabwe a bangarorin tattalin arziki da zaman takewa. (Fa’iza Mustapha)