logo

HAUSA

Tattalin arzikin zamani na Sin ya ninka har sau hudu cikin shekaru 10 da suka gabata

2022-07-04 10:34:04 CMG Hausa

Tattalin arzkin zamani na intanet na kasar Sin ya samu ci gaba cikin sauri a shekarun baya-bayan nan, inda ya karu daga yuan triliyan 11, kwatankwacin dala triliyan 1.65 a shekarar 2012, zuwa sama da yuan triliyan 45 a shekarar 2021.

Rahoton ma’aikatar kula da masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin ya nuna cewa, yawan tattalin arziki na zamani cikin alkaluman GDP na kasar, ya tashi daga kaso 21.6 zuwa kaso 39.8 bisa dari.

Kasar Sin ta gaggauta gina kayayyakin intanet. Zuwa karshen watan Mayun bana, ta gina ingantattun kayayyakin fasahohin zamani mafi girma a duniya, inda ta shimfida wayar sadarwa ta fibre-optic a dukkan birane tare da mallakar tashoshin tsarin sadarwa na 5G miliyan 1.7.

Haka kuma, kasar ta gaggauta hada tsarukan adana bayanai na Big Data da fasahar daidaita bayanai ta Cloud da fasahar AI da bangarorin samar da makamashi da kiwon lafiya da sufuri da ilimi da aikin gona. (Fa’iza Mustapha)